2 Chronicles 35:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ba a taɓa yin Bikin Ƙetarewa haka ba tun zamanin annabi Sama’ila; kuma babu sarkin Isra’ilan da ya taɓa yin irin Bikin Ƙetarewa kamar yadda Yosiya ya yi, tare da firistoci, Lawiyawa da kuma dukan Yahuda da Isra’ila, waɗanda suke can tare da mutanen Urushalima.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تُنْ زَامَانِنْ أَنَّبِے سَمَٰعِيلَ، بَعَتَٻَ يِنِرِنْ بِكٍ ڧٜىٰتَرٜىٰوَرْ نَنْبَ؞ بَابُ سَرْكِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ وَنْدَ يَتَٻَ بِكٍ ڧٜىٰتَرٜىٰوَ كَمَرْ يَدَّ يُواْسِيَا يَيِ دَ ڢِرِسْتُواْثِے دَ لَوِيَاوَا دَ دُكَنْ مَذَوْنَنْ عُرُوشَلِيمَ دَ مُتَنٜىٰ دَغَ دُكَنْ يَهُودَ دَ إِسْرَٰٓءِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba a taɓa yin Idin Ƙetarewa irin wannan ba tun kwanakin annabi Sama'ila, ba wani kuma daga cikin sarakunan Isra'ila da ya kiyaye Idin Ƙetarewa kamar yadda Yosiya ya kiyaye shi tare da firistoci, da Lawiyawa, da dukan mutanen Yahuza da na Isra'ila, waɗanda suke a wurin, da kuma mazaunan Urushalima.