2 Chronicles 35:21 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma Neko ya aiki ’yan saƙo ga Yosiya, yana cewa, “Me ya gama ni da kai, ya Sarkin Yahuda? Ban zo in yi yaƙi da kai ba. Na zo ne in yi yaƙi da gidan da yake gāba da ni! Ka ƙyale ni! Allah ne ya riga ya faɗa mini in hanzarta. Kada ka yi gāba da Allah, wanda yake tare da ni, don kada yă hallaka ka.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا سَرْكِے نٜىٰكُواْ يَتُورَ یَنْ عَيْكَ دَ سَڧُواْ وُرِنْ يُواْسِيَا ثٜىٰوَ «مٜىٰكَكٜىٰ نٜىٰمَ أَوُرِينَ، يَا سَرْكِنْ يَهُودَ؟ أَيْ، بَنْ ذُواْ إِنْيِ يَاڧِ دَكَيْ أَوَنَّنْ لُواْكَثِبَ؞ عَمَّا إِنَ كَيْ يَاڧِ غَ ڧَسَرْدَ تَكٜىٰ غَابَادَنِنٜىٰ؞ اللَّهْ كُمَ يَعُمَرْثٜىٰنِ إِنْيِ سَوْرِ؞ كَدَ كَيِ غَابَادَ اللَّهْ وَنْدَ يَكٜىٰ تَرٜىٰدَنِ، دُواْمِنْ كَدَ يَهَلَكَاكَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma Neko ya aika 'yan saƙo su faɗa masa su ce, “Me ya gama mu da juna, ya Sarkin Yahuza? Ban zo in yi yaƙi da kai ba. Na zo ne in yi yaƙi da Sarkin Assuriya! Ka ƙyale ni! Allah ne ya riga ya faɗa mini in hanzarta. Kada ka yi gāba da Allah, wanda yake tare da ni, don kada ya hallaka ka.”