2 Chronicles 36:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya tayar wa Sarki Nebukadnezzar, wanda ya sa ya yi rantsuwa da sunan Allah. Ya zama mai kunnen ƙashi da kuma taurin zuciya, bai kuwa juye ga Ubangiji, Allah na Isra’ila ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
صَدِڧِيَ يَيِ وَ سَرْكِے نٜىٰبُكَدْنٜىٰزَّرْ تَاوَيٜىٰ، وَنْدَ يَتِلَسْتَ شِ يَرَنْڟٜىٰ دَ سُونَنْ اللَّهْ ذَيْ يِمَسَ أَمِنْثِ؞ عَمَّا صَدِڧِيَ يَيِ تَوْرِنْ كَيْ دَ تَوْرِنْ ذُوثِيَا، يَڧِ يَتُوبَ يَجُويَ غَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya kuwa tayar wa sarki Nebukadnezzar wanda ya rantsar da shi da Allah. Amma ya ƙi kula, ya taurare zuciyarsa gāba da Ubangiji, Allah na Isra'ila.