2 Chronicles 36:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bugu da ƙari, dukan shugabannin firistoci da mutane suka ƙara zama marasa aminci, suna bin dukan abubuwan banƙyama na al’ummai, suka ƙazantar da haikalin Ubangiji, wanda ya tsarkake a Urushalima.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَنْدَ حَكَمَا، دُكَنْ مَنْيَنْ ڢِرِسْتُواْثِے دَ جَمَعَ، سُو مَا بَسُيِ أَمِنْثِبَ كُواْ كَطَنْ؞ سُنْيِ تَبِنْ أَبُبُوَنْ بَنْ ڨَمَ نَأَلْعُمَّيْ، سُنَ ڧَظَنْتَرْدَ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ وَنْدَ يَكٜىٰٻٜىٰ أَ عُرُوشَلِيمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dukan manyan firistoci da sauran jama'a gaba ɗaya, sun zama marasa aminci ƙwarai suna aikata dukan abubuwan banƙyama da al'ummai suke yi. Suka ƙazantar da Haikalin Ubangiji wanda ya tsarkake a Urushalima.