2 Chronicles 36:23 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ga abin da Sairus sarkin Farisa ya ce, “ ‘ Ubangiji Allah na sama, ya ba ni dukan mulkokin duniya, ya kuma naɗa ni in gina masa haikali a Urushalima a Yahuda. Duk wani na mutanensa a cikinku, bari yă haura yă tafi, bari kuma Ubangiji Allahnsa yă kasance tare da shi.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«غَا عُمَرْنِنْ سَرْكِے سَيِرُسْ نَ ڢَٰشِيَ؞ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نَسَمَ يَبَا نِے مُلْكٍ دُكَنْ مُلْكُواْكِنْ دُونِيَا؞ يَكُمَسَا نِے إِنْ غِنَا مَسَ غِدَا أَ عُرُوشَلِيمَ عَڧَسَرْ يَهُودَ؞ بَرِ دُكْ وَنْدَ يَكٜىٰ نَمُتَنٜىٰنْ يَهْوٜىٰهْ عَثِكِنْكُ يَكُواْمَ؞ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْسَ يَكَسَنْثٜىٰ تَرٜىٰ دَشِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ga shelar, “In ji Sairus Sarkin Farisa, Ubangiji, Allah na samaniya ya ba ni sarautar dukan duniya, ya kuma umarce ni in gina masa Haikali a Urushalima, ta ƙasar Yahuza. Duk wanda yake na mutanensa da suke nan, Ubangiji Allahnsa ya kasance tare da shi, bari ya haura zuwa can Urushalima.”