2 Chronicles 36:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yehohiyacin yana da shekara goma sha takwas sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima wata uku da kwana goma. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يٜىٰهُواْيَكِنْ يَنَدَ شٜىٰكَرَا تَݣُوسْ سَعَدَّ يَڢَارَ مُلْكِ، يَيِ مُلْكِ وَتَا عُكُ دَ ݣُونَ تَݣُوسْ أَ عُرُوشَلِيمَ؞ شِمَا يَعَيْكَتَ مُغُنْتَا سُواْسَيْ أَعِدُوانْ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yekoniya yana da shekara takwas sa'ad da ya ci sarauta, ya yi sarauta a Urushalima wata uku da kwana goma. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji.