2 Chronicles 5:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Babu wani abu a cikin akwatin alkawarin sai alluna biyu da Musa ya sa a cikinsa a Horeb, inda Ubangiji ya yi alkawari da Isra’ilawa bayan sun fito Masar.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَا وَنِ أَبُ عَثِكِنْ عَݣُوتِنْ، سَيْدَيْ أَلُّنَ بِيُ نَدُوڟٜىٰ وَطَنْدَ مُوسَٰى يَسَا عَثِكِنْ عَݣُوتِنْ عَبَبَّنْ تُدُنْ هُواْرٜىٰبْ، عِنْدَ يَهْوٜىٰهْ يَيِ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ دَ جَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ، سَعَدَّ سُكَ ڢِتُواْ دَغَ ڧَسَرْ مَصَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba kome cikin akwatin sai alluna biyu waɗanda Musa ya sa a ciki sa'ad da suke a Horeb. A Horeb ne Ubangiji ya ƙulla alkawarin da mutanen Isra'ila, sa'ad da suka fito daga Masar.