2 Chronicles 5:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dukan Lawiyawa waɗanda suke mawaƙa, Asaf, Heman, Yedutun da ’ya’yansu maza da dangoginsu, suka tsaya a gefen gabas na bagaden, saye da lilin mai kyau suna kuma kaɗa ganguna, garayu da molaye. Tare da su akwai firistoci 120 masu busan ƙahoni.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً دُكَنْ لَوِيَاوَنْ دَسُكٜىٰ مَوَاڧَ، وَتُواْ أَسَڢْ دَ هٜىٰمَنْ دَ يٜىٰدُتُنْ دَ یَیَنْسُ مَظَا دَ مَاتَا، تَرٜىٰدَ یَنْعُوَنْسُ سُكَسَا رِيغُنَنْ دَ عَكَيِ دَ لِيلِنْ مَيْݣَوْ؞ سُكَ ڟَيَ أَغَبَشِنْ بَغَدٜىٰنْ سُنَ تَبُغَ كُغٜىٰ، سُنَ كَطَ مُواْلُواْ دَ غَرَايَ؞ أَݣَويْ كُمَ ڢِرِسْتُواْثِے طَرِے دَ عَشِرِنْ مَاسُ بُوسَ كَكَكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dukan Lawiyawa mawaƙa, wato su Asaf, da Heman, da Yedutun tare da 'ya'yansu maza da 'yan'uwansu, aka sa su su tsaya a gabashin bagade, suna sāye da lilin mai kyau, suna ta kaɗa kuge, da molaye da garayu, ga kuma firistoci ɗari da ashirin masu busa ƙaho tare da su.