2 Chronicles 5:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan firistoci suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji zuwa wurinsa a ciki cikin wuri mai tsarki na haikali, Wuri Mafi Tsarki, suka sa shi ƙarƙashin fikafikan kerubobin.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ ڢِرِسْتُواْثِنْ سُكَ كَيْ عَݣُوتِنْ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ نَ يَهْوٜىٰهْ ذُوَا ثِكِ ثِكِنْ غِدَنْ؞ سُكَ كُوَ سَا شِ أَوُرِنْ ذَمَنْسَ ثِكِنْ وُرِے مَڢِے ڟَرْكِے، عَڧَرْڧَشِنْ ڢِكَڢِكَنْ حَلِتُّنَّنْ غُدَا بِيُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan firistoci suka shigar da akwatin alkawari na Ubangiji a wurinsa, wato a Wuri Mafi Tsarki na cikin Haikalin, a ƙarƙashin fikafikan kerubobi.