2 Chronicles 6:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Yanzu fa Ubangiji, Allah na Isra’ila, ka kiyaye wa bawanka Dawuda mahaifina alkawuran da ka yi masa sa’ad da ka ce, ‘Ba za ka kāsa kasance da mutumin da zai zauna a gabana a kan kujerar sarautar Isra’ila ba, in kawai ’ya’yanka maza za su kula cikin dukan abin da suke yi su yi tafiya a gabana bisa ga dokata, kamar yadda ka yi.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«يَنْذُ يَا يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ، بَرِ كَثِكَ أَلْڧَوَرِنْدَ كَيِ وَبَاوَنْكَ بَابَنَ دَاوُدَ دَ كَثٜىٰ مَسَ، ‹عِدَنْ یَیَنْكَ مَظَا ذَاسُ لُورَ دَ رَايُوَرْسُ، سُكُمَيِ تَڢِيَ تَرٜىٰدَنِ كَمَرْ يَدَّ كَيْ كَيِ، تُواْ، كُلُّمْ ذَاعَ سَامِ وَنِ دَغَ ثِكِنْ عِيَلِنْكَ دَ ذَيْ غَاجِ كُجٜىٰرَرْ مُلْكٍ إِسْرَٰٓءِيلَ؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yanzu fa, ya Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka cika alkawarin da ka yi wa bawanka tsohona cewa, ‘Daɗai, ba za a rasa wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba, in dai 'ya'yanka maza za su lura da al'amuransu, don su yi tafiya bisa ga shari'ata, yadda kai ka yi tafiya a gabana.’