2 Chronicles 6:23 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
sai ka ji daga sama ka kuma yi wani abu. Ka shari’anta tsakanin bayinka, kana sāka wa mai laifi ta wurin kawo a kansa hakkin abin da ya yi. Ka nuna cewa marar laifi ba shi da laifi, ta haka a fiffita rashin laifinsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَا يَهْوٜىٰهْ ، سَيْكَجِ دَغَ سَمَ؞ كَيِ وَبَايِنْكَ شَرِيعَ؞ كَحُكُنْتَ مَيْ لَيْڢِے، كَمَيْدَ لَيْڢِنْسَ عَكَنْسَ؞ مَيْ غَسْكِيَ كُمَ كَنُونَ شِے مَرَرْ لَيْڢِے نٜىٰ بِسَغَ غَسْكِيَرْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
sai ka ji ka yi wa bayinka shari'a daga Sama, ka hukunta wa mugun, ka ɗora masa alhakinsa, ka baratar da adalin, ka ba shi sakayyar adalcinsa.