2 Chronicles 6:27 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
sai ka ji daga sama ka kuma gafarta zunubin bayinka, mutanenka Isra’ila. Ka koya musu hanyar da ta dace da za su yi zama, ka kuma aika ruwan sama a ƙasar da ka ba mutanenka gādo.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ كَجِ دَغَ سَمَ؞ كَغَاڢَرْتَ ذُنُبَنْ بَايِنْكَ وَتُواْ جَمَعَرْكَ إِسْرَٰٓءِيلَ؞ كَكُواْيَ مُسُ حَنْيَرْ رَايُوَا مَيْݣَوْ وَدَّ ذَاسُبِے؞ سَعَنً، يَا يَهْوٜىٰهْ ، كَعَيْكَ دَ ضُوً سَمَ عَڧَسَرْدَ كَبَا مُتَنٜىٰنْكَ تَذَمَ ڧَسَرْسُ تَغَادُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
sai ka ji daga Sama ka gafarta zunubin bayinka, wato jama'arka Isra'ila, lokacin da ka koya musu kyakkyawar hanya da za su bi. Sai ka sa a yi ruwa a ƙasarka, wadda ka ba jama'arka gādo.