2 Chronicles 7:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A rana ta ashirin da uku na watan bakwai sai ya sallami mutane su tafi gidajensu da farin ciki da kuma murna a zuciya saboda abubuwa masu kyau da Ubangiji ya yi domin Dawuda da Solomon da kuma domin mutanensa Isra’ila.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ رَانَ تَعَشِرِنْ دَ عُكُ غَ وَتَنْ بَݣَويْ، سُلَيْمَٰنُ يَسَلَّمِ جَمَعَ سُكُواْمَ غِدَاجٜىٰنْسُ؞ جَمَعَ سُكَ تَڢِے دَ ڢَضٍ ثِكِ دَ مُرْنَ أَ ذُوثِيَارْسُ سَبُواْدَ أَلْحٜىٰرِنْ دَ يَهْوٜىٰهْ يَنُونَاوَ دَاوُدَ دَ سُلَيْمَٰنُ دَ كُمَ مُتَنٜىٰنْسَ إِسْرَٰٓءِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A ran ashirin da uku ga watan bakwai, sai sarki ya sallami jama'a su koma gidajensu, suna ta murna da farin ciki a zuciyarsu saboda alherin da Ubangiji ya nuna wa Dawuda, da Sulemanu, da kuma jama'arsa Isra'ila.