2 Chronicles 7:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mutane za su amsa, ‘Domin sun yashe Ubangiji Allah na kakanninsu, wanda ya fitar da su daga Masar, suka rungumi waɗansu alloli, suna musu sujada, suna bauta musu, shi ya sa ya kawo dukan wannan masifa a kansu.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰ ذَاسُ أَمْسَ مُسُ سُثٜىٰ، ‹أَيْ، سَبُواْدَ سُنْڧِے يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْسُ وَنْدَ يَڢِتَرْ دَسُو دَغَ ڧَسَرْ مَصَرْ نٜىٰ؞ سُكَ جُويَا سُكَبِے وَطَنْسُ أَلُّواْلِ سُنَيِ مُسُ سُجَّدَ؞ شِيَسَا يَهْوٜىٰهْ يَكَٰوُاْ وَنَّنْ مَسِيڢَ عَكَنْسُ؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Sa'an nan kuma za su ce, ‘Saboda sun rabu da Ubangiji, Allah na kakanninsu, wanda ya fitar da su daga ƙasar Masar, amma suka bi waɗansu gumaka, suka yi musu sujada, suka bauta musu, saboda haka ne ya aukar musu da duk wannan bala'i.’ ”