2 Chronicles 7:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da dukan Isra’ilawa suka ga wutar na saukowa, ɗaukakar Ubangiji kuma tana a bisa haikalin, sai suka durƙusa a dakali da fuskokinsu a ƙasa, suka yi sujada suka kuma yi godiya ga Ubangiji suna cewa, “ Ubangiji mai alheri ne, ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ دُكَنْ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا سُكَغَ سَوْكُواْوَرْ وُتَادَ طَوْكَكَرْ يَهْوٜىٰهْ عَكَنْ غِدَنْسَ، سَيْ سُكَ رُسُنَ دَ ڢُسْكُواْكِنْسُ حَرْ ڧَسَا، سُنَ يَبُوانْ يَهْوٜىٰهْ سُنَ ثٜىٰوَ «يَهْوٜىٰهْ مَيْ أَلْحٜىٰرِ نٜىٰ، ڧَوْنَرْسَ مَرَرْ ثَنْجَاوَا تَهَرْ أَبَدَاثٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da dukan Isra'ilawa suka ga wuta ta sauko daga sama, ɗaukakar Ubangiji kuma na cike da Haikalin, sai suka sunkuyar da kansu ƙasa, suka yi sujada, suka yabi Ubangiji, saboda nagarinsa da madawwamiyar ƙaunarsa.