2 Chronicles 7:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sarki Solomon kuwa ya miƙa hadayar bijimai dubu ashirin da biyu da kuma tumaki da awaki dubu ɗari da dubu ashirin. Ta haka sarki da dukan mutane suka keɓe haikalin Allah.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے سُلَيْمَٰنُ يَمِيڧَ هَدَايَرْ بِجِمَيْ دُبُو عَشِرِنْ دَ بِيُ دَ أَوَكِ دُبُو طَرِے دَ عَشِرِنْ؞ تَهَكَ سَرْكِے دَ دُكَنْ مُتَنٜىٰ سُكَ كٜىٰٻٜىٰ غِدَنْ اللَّهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sarki Sulemanu kuwa ya miƙa hadayar bijimai dubu ashirin da dubu biyu (22,000), da tumaki dubu ɗari da dubu ashirin (120,000). Ta haka sarki tare da dukan jama'a suka keɓe Haikalin Allah.