2 Chronicles 9:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
(Mutanen Hiram da mutanen Solomon suka kawo zinariya daga Ofir, suka kuma kawo gungumen algum da duwatsu masu daraja.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مَاسُ تُوڧِنْ جِضَاغٜىٰنْ ضُوً حِرَمْ كُوَ تَرٜىٰدَ مَعَيْكَتَنْ سُلَيْمَٰنُ سُكَ كَٰوُاْ ظِينَارِيَ مَڢِے ݣَوْ دَغَ عُواْڢِرْ؞ سُكَ كُمَ كَٰوُاْ كَتَكَنْ إِتَاثٜىٰنْ أَلْغُمْ دَيَوَ دَ دُوَڟُو مَاسُ دَرَجَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bayan haka kuma barorin Hiram tare da barorin Sulemanu waɗanda suka kawo zinariya daga Ofir, sun kuma kawo itatuwan algum da duwatsu masu daraja.