2 Chronicles 9:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sarki yana da jerin jiragen ruwa na kasuwanci waɗanda mutanen Hiram ne suke kula da su. Sau ɗaya kowace shekara uku sukan dawo ɗauke da zinariya, azurfa, hauren giwa, gogo da kuma birai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے يَنَدَ جِضَاغٜىٰنْ ضُوَ مَاسُبِنْ تٜىٰكُ سُنَ كَاسُوَنْثِ تَرٜىٰدَ جِضَاغٜىٰنْ ضُوَ نَ سَرْكِے حِرَمْ؞ كُواْوَثٜىٰ شٜىٰكَرَا عُكُ، جِضَاغٜىٰنْ سُكَنْ دَاوُاْ دَ ظِينَارِيَ دَ أَظُرْڢَا دَ هَڧُواْرِنْ غِيوَ دَ بِرَيْ مَنْيَ دَ ڧَنَانَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sau ɗaya a shekaru uku, sarki yakan aika da jiragen ruwa zuwa Tarshish tare da barorin Hiram, su kawo zinariya, da azurfa, da hauren giwa, da manyan birai, da ɗawisu.