2 Chronicles 9:27 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sarki ya sa azurfa ta zama barkatai a Urushalima kamar duwatsu, al’ul kuma da yawa kamar itatuwan fir a gindin tsaunuka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے يَسَا أَظُرْڢَا تَذَمَ أَبِنْ بَنْظَ كَمَرْ دُوَڟُو ثِكِنْ عُرُوشَلِيمَ، يَكُمَسَا إِتَاثٜىٰنْ سٜىٰدَ سُيِيَوَ كَمَرْ عِتَتُوَنْ ٻَوْرٜىٰ عَيَنْكِنْ ڧأَنَانً تُدَّيْ نَ يَهُودَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sarki ya sa azurfa ta gama gari, kamar duwatsu a Urushalima, ya kuma sa itatuwan al'ul su yalwata kamar itatuwan ɓaure a Shefela.