2 Chronicles 9:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma ban gaskata abin da suka faɗa ba sai da na zo na kuma gani da idanuna. Tabbatacce, ko rabin girman hikimarka ba a faɗa mini ba, ka wuce labarin da na ji nesa ba kusa ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا بَنْ غَسْكَتَ لَابَرِنْسُ بَ، سَيْ دَ نَذُواْ نَغَنِ دَ عِدَنُونَ؞ أَشٜىٰ! كُواْ رَبِے مَا بَعَڢَطَا مِنِ بَ! لَلَّيْ حِكِمَرْكَ دَ أَرْزِڧِنْكَ سُنْڢِے أَبِنْدَ نَجِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma dā ban gaskata labarinsu ba, sai da na zo na gani da idona, ashe, ko rabin yawan hikimarka ma ba a faɗa mini ba. Ashe, duk labarin da aka faɗa mini, ka zarce haka ƙwarai.