2 Chronicles 9:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ji daɗi a cikinka ya sa ka a kan kujerar sarautarsa a matsayin sarki don ka yi mulkin domin Ubangiji Allahnka. Saboda ƙaunar Allahnka wa Isra’ila da kuma sha’awarsa na riƙe su har abada, ya naɗa ka sarki a bisansu, don ka yi adalci da kuma gaskiya.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَلْبَرْكَ تَا تَبَّتَا غَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكَ، وَنْدَ يَجِ دَاطِنْكَ حَرْ يَسَاكَ عَكُجٜىٰرَرْ مُلْكٍ إِسْرَٰٓءِيلَ دُواْمِنْ كَيِ مُلْكِ أَ سُونَنْسَ! سَبُواْدَ اللَّهْ نْكَ يَنَ ڧَوْنَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ، كُمَ يَنَ سُواْ يَكَڢَسُ حَرْ أَبَدَانٜىٰ، شِے يَسَا يَنَطَكَ سَرْكِے دُواْمِنْ كَيِ شَرِيعَ ثِكِنْ غَسْكِيَ دَ أَدَلْثِے؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka wanda yake murna da kai, wanda ya hawar da kai gadon sarautarsa, don ka zama sarki a gaban Ubangiji Allahnka. Gama Allah yana ƙaunar Isra'ila, zai kuwa tabbatar da su har abada, shi ya sa ya naɗa ka sarkinsu, don ka aikata gaskiya da adalci.”