2 Corinthians 1:19 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Gama Ɗan Allah, Yesu Kiristi, wanda ni da Sila da Timoti muka yi muku wa’azinsa, ai, ba “I” da “A’a” ba ne, amma a cikin Kiristi, “I” ne kullum.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُواْمِنْ طَنْ اللَّهْ عِيسَىٰ أَلْمَسِيحُ ، وَنْدَ نِے دَ سِيلَ دَ تِمُواْتِ مُكَيِ مُكُ وَعَظِنْسَ، أَيْ، بَوَنِ مَيْ «عِ» دَ «أَعَ» بَنٜىٰ، عَمَّا عَثِكِنْسَ «عِ» نٜىٰ كُلُّمْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Domin kuwa, Ɗan Allah, Yesu Almasihu, wanda ni, da Sila, da Timoti muka yi muku wa'azi, ai, ba shiririta a game da shi, har kullum a kan gaskiya yake.