2 Corinthians 10:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ba za mu yi ƙarfin halin lissafta kanmu, ko mu kwatanta kanmu da waɗansu masu yabon kansu ba. Sa’ad da suke gwada kansu da kansu, da kuma kwatanta kansu da kansu, ba su da hikima.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَنٜىٰ مُو! أَيْ، بَمُ إِسَ مُڠُودَ، كُواْ مُطَوْكِ كَنْمُ كَمَرْ مُتَنٜىٰنْ دَسُكٜىٰ غَنِ سُنْڢِے كُواْوَبَ؞ سُو وَطَنَّنْ مُتَنٜىٰ مَاسُ عَوْنَ كَنْسُ دَ جُونَ، سُنَ كُمَ نٜىٰمَنْ بَمْبَنْثِ ڟَكَانِنْسُ دَ جُونَ، سُو وَوَيٜىٰنٜىٰ!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wane mu mu daidaita kanmu, ko mu gwada kanmu da waɗansu masu yabon kansu! Ashe, waɗannan mutane masu auna kansu da juna, suna kuma neman bambanci a tsakaninsu da juna, ba su da basira.