2 Corinthians 11:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sau uku aka bulale ni da bulalar ƙarfe, sau ɗaya aka jajjefe ni da duwatsu, sau uku jirgin ruwa ya ragargaje ina ciki, na kwana na kuma yini ruwan teku yana tafiya da ni.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَوْ عُكُ حُكُمَرْ رُواْمَاوَا سُكَيِ مِنِ بُلَلَ؞ أَنْ كُمَ تَٻَ جٜىٰجّٜىٰڢٜىٰنِ دَ دُوَڟُو سَوْ طَيَ؞ سَوْ عُكُ جِضَاغٜىٰنْ ضُوَ سُنْ ڢَرْڢَشٜىٰ إِنَ ثِكِ؞ نَكُمَ تَٻَ ݣُونَ حَرْ نَا يِنِ عَثِكِنْ تٜىٰكُ، كَاڢِنْ عَكَذُواْ عَكَ ثِرٜىٰنِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sau uku aka bulale ni da tsumagu, sau ɗaya har aka jejjefe ni da dutse. Sau uku jirgi ya ragargaje ina ciki, na kwana na yini ruwan bahar yana tafiya da ni.