2 Corinthians 11:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da nake tare da ku kuma nake zaman rashi, ban nawaita wa kowa ba, gama ’yan’uwan da suka zo daga Makidoniya sun biya bukata. Na kiyaye kaina daga nawaita muku ta kowace hanya, zan kuma ci gaba da yin haka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
لُواْكَثِنْ دَ نَكٜىٰ تَرٜىٰدَكُو، إِنَدَ بُڧَاتَرْ كُطِ، دُكْدَهَكَ بَنْ دَامٜىٰكُبَ؞ یَنْعُوَ مَاسُبِے وَطَنْدَ سُكَذُواْ دَغَ مَكِدُواْنِيَ نٜىٰ سُكَ كَٰوُاْ مِنِ دُكْ أَبِنْدَ نَكٜىٰ بُڧَاتَ؞ بَنْ طُواْرَ مُكُ نَوْيِ أَ لُواْكَثِنْ بَ، كُمَ ذَنْ ثِيغَبَدَ يِنْهَكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da nake a wurinku kuma nake zaman rashi, ban nauyaya wa kowa ba, domin 'yan'uwan da suka zo daga Makidoniya su ne suka biya mini bukata. Saboda haka, na ƙi nauyaya muku ta kowace hanya, ba kuwa zan nauyaya muku ba.