2 Corinthians 12:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ نَغَمْسُ دَ رَشِنْ ڧَرْڢِينَ دَ ثِنْمُتُنْثِنْ دَ عَكٜىٰيِمِنِ دَ شَنْ وَهَلَ دَ ڟَنَنِ دَ مَسِيڢُ سَبُواْدَ أَلْمَسِيحُ ؞ غَمَا سَعَدَّ إِنَدَ رَشِنْ ڧَرْڢِے، أَ لُواْكَثِنْ نٜىٰ نَكٜىٰ دَ ڧَرْڢِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Saboda haka, ina murna da raunanata, da cin mutuncin da ake yi mini, da shan wuya, da shan tsanani, da masifu saboda Almasihu, don sa'ad da nake rarrauna, a sa'an nan ne nake da ƙarfi.