2 Corinthians 12:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُواْمِنْ كَدَ إِنْكُمَيِ تَاڧَمَ دَ وَطَنَّنْ رُعُيَ مَڢِے بَنْ مَامَاكِ، سَيْ أَنْعَيْكُواْ مِنِ وَتَ ثُوتَرْ دَ تَذَمَ مِنِ ڧَيَ أَجِكِے؞ وَنَّنْ يَذَمَ طَنْ عَيْكَ نٜىٰ وَنْدَ شَيْطَنْ يَعَيْكُواْ دُواْمِنْ يَدِنْغَ بَانِ وَهَلَ يَكُمَ هَنَنِ طَغَ كَيْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Don kada kaina yă kumbura kuma saboda mafifitan wahayan da aka yi mini, sai aka saka mini wata cuta, wadda ta zama mini ƙaya, jakadan Shaiɗan, don yă riƙa wahalshe ni, don kada kaina ya kumbura.