2 Corinthians 5:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ba ƙoƙari muke mu yabe kanmu a gare ku ba ne, sai dai muna ba ku damar yin taƙama da mu ne, don ku sami amsar da za ku ba wa waɗanda suke taƙama da abin da ake gani ne, a maimakon abin da yake cikin zuciya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَوَيْ مُنَ سُواْ مُيَبِے كَنْمُ أَغَبَنْكُ بَنٜىٰ، سَيْدَيْ مُنَ ڧُواْڧَرِ مُبَاكُ دَلِيلِ مَيْݣَوْنٜىٰ وَنْدَ ذَاكُجِ دَاطِنْمُ، دُوانْ كُإِيَ بَادَ أَمْسَ غَ وَطَنْدَ سُكٜىٰ طَغَ كَيْ سَبُواْدَ مَڟَيِنْسُ، أَمَيْمَكُوانْ حَلِنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Har wa yau kuma, ba yabon kanmu muke yi a gare ku ba, sai dai muna ba ku hanyar yin taƙama da mu, don ku sami yadda za ku mai da jawabi ga waɗanda suke fariya da maƙaminsu, ba da halinsu ba.