2 Corinthians 9:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Gama in waɗansu mutanen Makidoniya sun zo tare da ni, suka tarar ba a shirye kuke ba, kunya ta ishe mu, balle fa ku, saboda amincewa da muke yi da ku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ عِدَنْ نَا ذُواْ تَرٜىٰدَ وَطَنْسُ مَاسُبِے دَغَ مَكِدُواْنِيَ، بَانَ سُواْ سُذُواْ سُسَامُ بَكُ رِغَا كُنْ شِرْيَ تَيْمَكُوانْكُبَ؞ إِنْ حَكَ يَڢَرُ، ذَنْشَا كُنْيَا سَبُواْدَ يَوَنْ تَاڧَمَرْدَ نَيِ عَكَنْكُ، بَنِ كَطَيْ ذَنْشَا كُنْيَرْبَ، هَرْمَا دَكُو؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Don kada ya zamana in waɗansu mutanen Makidoniya sun zo tare da ni, suka tarar ba ku shirya ba, kunya ta ishe mu, balle fa ku, saboda amincewa da muke yi da ku.