2 Kings 1:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Iliya ya ce masa, “In ni mutumin Allah ne, bari wuta tă sauko daga sama tă cinye ka da sojojinka hamsin!” Sai wuta ta sauko daga sama ta cinye kaftin tare da sojojinsa hamsin.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِلْيَاسُ يَأَمْسَ يَثٜىٰ مَسَ «عِدَنْ نِے مُتُمِنْ اللَّهْ نٜىٰ، بَرِ وُتَا تَسَوْكُواْ دَغَ سَمَ تَثِنْيٜىٰكَ دَ سُواْجُواْجِنْكَ حَمْسِنْ؞» نَنْ دَ نَنْ سَيْ وُتَا تَسَوْكُواْ دَغَ سَمَ تَثِنْيٜىٰ بَبَّنْ سُواْجَنْ دَ ڧُنْغِيَرْ سُواْجُواْجِنْسَ حَمْسِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Iliya ya ce wa shugaban da mutum hamsin ɗin, “Idan ni mutumin Allah ne, bari wuta ta sauko daga sama ta cinye ka da mutane naka hamsin.” Wuta kuwa ta sauko daga sama, ta cinye shugaban tare da mutanensa hamsin.