2 Kings 1:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka sai sarki ya aiki kaftin na uku da sojojinsa hamsin. Wannan kaftin na ukun ya haura ya durƙusa a gaban Iliya, ya roƙe shi ya ce, “Mutumin Allah, ina roƙonka ka dubi darajar raina da na waɗannan sojoji hamsin, bayinka!
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَوْ نَعُكُ سَيْ سَرْكِے يَسَاكٜىٰ عَيْكَ دَ وَنِ بَبَّنْ سُواْجَ دَ ڧُنْغِيَرْ سُواْجُواْجِ حَمْسِنْ؞ سَيْ يَهَوْرَ تُدُنْ، يَدُرْڧُسَ أَغَبَنْ إِلْيَاسُ يَضُواْڧٜىٰشِ يَثٜىٰ «يَا مُتُمِنْ اللَّهْ ، كَيِ مِنِ جِنْڧَيْ دَنِے دَ ڧُنْغِيَرْ سُواْجُواْجِنَ؞ بَرِ كَغَ دَرَجَرْ رَيْنَ دَ نَوَطَنَّنْ بَايِنْكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sarki kuma ya sāke aiken wani shugaba, na uku ke nan, tare da mutanensa hamsin. Sai shugaba na uku ya tafi ya rusuna a gaban Iliya, ya roƙe shi, ya ce, “Ya mutumin Allah, ina roƙonka ka ga darajar raina da na barorinka, su hamsin.