2 Kings 10:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Nan da nan sa’ad da Yehu ya gama yin hadayar, sai ya umarci masu gadin da hafsoshi, “Ku shiga ku karkashe su; kada ku bar wani yă tsere.” Saboda haka suka karkashe su da takobi. Masu gadin da hafsoshin suka wuwwurga gawawwakinsu waje, suka kuma shiga ciki cikin haikalin Ba’al ɗin,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَظَرَرْ يَغَمَ مِيڧَ هَدَايَ، سَيْيَڢِتَ يَثٜىٰ وَمَاسُ غَادِ دَ مَنْيَنْ سُواْجُواْجِ «كُشِغَ مَظَا كُكَكَّشٜىٰسُ دُكَ؞ كَدَ كُيَرْدَ وَنِ يَكُٻُثٜىٰ!» سُكَ كَشٜىٰسُ دَ تَكُواْبِے سُكَجٜىٰڢَرْ دَ جِكُنَنْسُ وَجٜىٰ؞ سَعَنً سُكَ شِغَ ثِكِ ثِكِنْ غِدَنْ بَعَلْ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Nan da nan da Yehu ya gama miƙa hadaya ta ƙonawa, sai ya ce wa mai tsaro da shugabannin, “Ku shiga, ku karkashe su, kada ku bar wani ya tsere.” Da suka karkashe su, sai suka fitar da su waje, sa'an nan suka shiga can cikin haikalin Ba'al.