2 Kings 10:30 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ubangiji ya ce wa Yehu, “Tun da yake ka aikata abin da yake mai kyau a idanuna, ka kuma yi wa gidan Ahab dukan abin da yake a zuciyata, ina yin maka alkawari cewa zuriyarka za su yi mulkin Isra’ila har tsara ta huɗu.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يَهْوٜىٰهْ يَثٜىٰ وَ يٜىٰهُو «تُنْدَيَكٜىٰ كَا عَيْكَتَ أَبِنْدَ يَكٜىٰ مَيْݣَوْ غَ عِدَنُونَ، كَكُمَيِ وَغِدَنْ أَهَبْ دُكَنْ أَبِنْدَ يَكٜىٰ أَ ذُوثِيَاتَ، إِنَ يِمَكَ أَلْڧَوَرِ ثٜىٰوَ ذُرِيَرْكَ ذَاسُيِ مُلْكٍ إِسْرَٰٓءِيلَ حَرْ ڟَارَا تَهُطُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji kuwa ya ce wa Yehu, “Da yake ka yi abin da yake daidai a gare ni, ka yi wa gidan ahab bisa ga dukan abin da yake a zuciyata, 'ya'yanka, har tsara ta huɗu, za su ci sarautar Isra'ila.”