2 Kings 10:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da wasiƙar ta iso, sai mutanen nan suka ɗauki dukan ’ya’yan sarkin nan saba’in, suka kashe su, suka sa kawunansu cikin kwanduna, suka aika wa Yehu a Yezireyel.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ وَسِيڧَرْ تَذُواْ حَنُّنْسُ، سَيْ سُكَ كَكَّامَ یَیَ مَذَنْ سَرْكِے غُدَا سَبَعِنْ سُكَ كَكَّشٜىٰ، سُكَ ثِثِّرٜىٰ كَوُنَنْسُ سُكَسَا عَݣُونْدُواْ سُكَ عَيْكَ وَ يٜىٰهُو أَ يٜىٰظِرٜىٰيٜىٰلْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da wasiƙar ta iso wurinsu, sai suka kwashi 'ya'yan sarki guda saba'in, suka karkashe su. Suka sa kawunansu cikin kwanduna, suka aika wa Yehu a Yezreyel.