2 Kings 11:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da ta duba sai ga sarki, tsaye kusa da ginshiƙi, bisa ga al’ada. Hafsoshi da masu busa suna tsaye kusa da sarki, dukan mutanen ƙasar kuma suna farin ciki suna busa ƙahoni. Sai Ataliya ta keta tufafinta ta tā da murya tana cewa, “Kai! Wannan cin amana ne! Ai, wannan cin amana ne!”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ تَدُوبَ، سَيْ تَغَ سَابُوانْ سَرْكِے ڟَيٜىٰ كُسَدَ غِنْشِڧِنْ غِدَنْ، بِسَغَ أَلْعَادَرْ نَطَوَرْ سَرْكِے؞ تَا كُمَ غَ مَنْيَنْ سُواْجُواْجِ دَ مَاسُ بُوسَ كَكَكِ سُنَ ڟَيٜىٰ كُسَدَ سَرْكِنْ دَ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ ڧَسَرْ سُنَ كِرَرِ سُنَ بُوسَ كَكَكِ دَ ڢَضٍ ثِكِ سُواْسَيْ؞ سَيْ أَتَلِيَ تَيَيَّاغٜىٰ رِيغُنَنْتَ تَيِ إِيهُ تَنَ ثٜىٰوَ «كَيْ! ثِنَمَنَ نٜىٰ! أَيْ، وَنَّنْ ثِنَمَنَ نٜىٰ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da ta duba, sai ta ga sarki a tsaye kusa da ginshiƙi bisa ga al'ada, shugabanni da masu busa kuwa suna tsaye kusa da sarki. Dukan mutanen ƙasar suna ta murna suna ta busa ƙaho. Sai Ataliya ta kece tufafinta, ta yi ihu, tana cewa, “Tawaye, tawaye!”