2 Kings 11:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai dukan mutanen ƙasar suka tafi haikalin Ba’al suka rushe shi. Suka farfasa bagadai da kuma gumaka, suka kuma kashe Mattan wanda yake firist na Ba’al a gaban bagade. Sa’an nan Yehohiyada firist ya sa matsara a haikalin Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ ڧَسَرْ سُكَ تَڢِے غِدَنْ بَعَلْ، سُكَ رُشٜىٰشِ؞ سُكَ كُمَ رُشٜىٰ بَغَدٜىٰنْ، سُكَ ڢَرْڢَشٜىٰ صِڢُّواْڢِنْ غُمَكَنْسَ؞ سَعَنً سُكَ كَشٜىٰ ڢِرِسْتِ نَ بَعَلْ مَيْ سُونَ مَتَّنْ أَغَبَنْ بَغَدٜىٰنْ بَعَلْ؞ يٜىٰهُواْيِدَ ڢِرِسْتِ يَسَا مَاسُ غَادِ سُيِ غَادِنْ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai dukan jama'ar ƙasa suka tafi haikalin Ba'al suka farfashe shi, da bagadensa da siffofinsa. Suka kuma kashe Mattan firist na Ba'al a gaban bagaden. Yehoyada kuwa ya sa matsara su yi tsaron Haikalin Ubangiji,