2 Kings 11:19 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya tafi tare da komandodin sojoji, Keretawa, matsara da kuma dukan mutanen ƙasar, tare kuwa suka kawo sarki daga haikalin Ubangiji zuwa cikin fada, ta ƙofar matsara. Sarki kuwa ya ɗauki mazauninsa a bisa kursiyin sarauta,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً يٜىٰهُواْيِدَ دَ مَنْيَنْ سُواْجُواْجِ دَ سُواْجُواْجِ مَاسُ غَادِنْ سَرْكِے دَ مَاسُ غَادِنْ غِدَنْ سَرْكِے دَ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ ڧَسَرْ سُكَيِ وَ سَرْكِے يُواْوَشْ رَكِيَ دَغَ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ذُوَا غِدَنْ سَرْكِے؞ سُكَ شِغَرْدَ سَرْكِے تَ ڧُواْڢَرْ مَاسُ غَادِ ذُوَا ثِكِنْ غِدَنْسَ؞ سَيْ سَرْكِے يَهَوْ كُجٜىٰرَرْ مُلْكِ يَذَوْنَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
ya kuma sa shugabanni, da Keretiyawa, da matsara, da dukan jama'ar ƙasar, su fito da sarki daga Haikalin Ubangiji, suka rufa masa baya ta ƙofar matsara zuwa gidan sarki. Suka sa shi a gadon sarautar sarakuna.