2 Kings 12:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A wannan lokaci, Hazayel sarkin Aram ya haura, ya kai wa Gat hari, ya kuma ci ta da yaƙi. Sa’an nan ya juya don yă yaƙi Urushalima.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ لُواْكَثِنَّنْ، سَرْكِے هَظَيٜىٰلْ نَ سُورِيَ يَهَوْرَ يَڢَاطَوَ بِرْنِنْ غَتْ دَ يَاڧِ، يَيِ نَصَرَا؞ سَعَنً يَنُڢَ يَكَيْ وَ عُرُوشَلِيمَ يَاڧِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Hazayel Sarkin Suriya kuwa ya tafi ya yi yaƙi da Gat har ya cinye ta, ya kuma shirya zai yi yaƙi da Urushalima.