2 Kings 12:21 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Hafsoshin da suka kashe shi kuwa su ne Yozabad ɗan Shimeyat da Yehozabad ɗan Shomer. Ya mutu, aka kuma binne shi tare da kakanninsa a Birnin Dawuda. Sai Amaziya ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَتَّاوَنْسَ وَطَنْدَ سُكَ كَشٜىٰشِ سُونٜىٰ، يُواْظَكَرْ طَنْ شِمٜىٰيَتْ دَ يٜىٰهُواْظَبَدْ طَنْ شُواْمٜىٰرْ؞ عَكَ بِنّٜىٰشِ تَرٜىٰدَ كَاكَنِّنْسَ عَبِرْنِنْ دَاوُدَ؞ سَيْ أَمَظِيَ طَنْسَ يَغَاجٜىٰشِ يَذَمَ سَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yozakar ɗan Shimeyat, da Yehozabad ɗan Shemer su ne fādawansa da suka kashe shi. Aka binne shi a makabartar kakanninsa cikin birnin Dawuda. Amaziya ɗansa ya gāji sarautarsa.