2 Kings 12:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yehohiyada firist ya ɗauki akwatin ya huda rami a murfinsa. Ya ajiye shi kusa da bagade a hannun dama na haikalin Ubangiji. Firistocin da suke tsaron ƙofar suka zuba dukan kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji a cikin akwatin.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً يٜىٰهُواْيِدَ يَطَوْكِ عَݣُوتِ، يَسَا رَامِ أَ مُرْڢِنْ يَأَجِيٜىٰ عَݣُوتِنْ كُسَدَ بَغَدٜىٰنْ، أَ حَنُّنْ دَامَ عِدَنْ مُتُمْ يَنَ شِغَ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞ ڢِرِسْتُواْثِے مَاسُ غَادِنْ ڧُواْڢَرْ غِدَنْ، سُكَسَا دُكَنْ كُطَطٜىٰنْ دَ عَكَ كَٰوُاْ ثِكِنْ عَݣُوتِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Yehoyada, firist, ya ɗauki akwati, ya huda rami a murfin, sa'an nan ya ajiye shi kusa da bagade a sashin dama na shiga Haikalin Ubangiji. Firistocin da suke tsaron ƙofar suka saka dukan kuɗin da aka kawo a Haikalin Ubangiji.