2 Kings 13:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A shekara ta ashirin da uku ta Yowash ɗan Ahaziya, sarkin Yahuda, Yehoyahaz ɗan Yehu, ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuwa yi mulki shekaru goma sha bakwai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَثِكِنْ شٜىٰكَرَا تَعَشِرِنْ دَ عُكُ تَمُلْكٍ سَرْكِے يُواْوَشْ طَنْ أَهَظِيَ نَ يَهُودَ، يٜىٰهُواْوَهَظْ طَنْ يٜىٰهُو يَڢَارَ مُلْكٍ إِسْرَٰٓءِيلَ أَ سَمَرِيَ؞ يَيِ مُلْكِ شٜىٰكَرَا غُواْمَشَا بَݣَويْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A shekara ta ashirin da uku ta sarautar Yowash ɗan Ahaziya Sarkin Yahuza, Yehowahaz ɗan Yehu ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara goma sha bakwai.