2 Kings 13:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai ya ce wa Yehowash sarkin Isra’ila, “Ka ɗauki baka a hannunka.” Da ya ɗauka, sai Elisha ya sa hannunsa a hannuwan sarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ أَلْيَسَعَ يَثٜىٰ وَسَرْكِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ «جَا بَكَنْكَ دُوانْ كَيِ هَرْبِے؞» سَيْ يَجَا بَكَنْ؞ سَعَنً أَلْيَسَعَ يَسَا حَنُّنْسَ عَكَنْ حَنُّنْ سَرْكِے يٜىٰهُواْوَشْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan ya ce, “Ka buɗe tagar da take wajen gabas.” Sai ya buɗe. Elisha ya kuma ce masa, “Ka ja bakan.” Ya kuwa ja. Sai Elisha ya ɗora hannuwansa a bisa hannuwan sarki. Sa'an nan Elisha ya ce, “Harba.” Sai ya harba. Elisha kuwa ya ce, “Kibiyar Ubangiji ta nasara, kibiyar nasara a kan Suriya. Gama za ka yi yaƙi da Suriyawa a Afek har ka ci su.”