2 Kings 13:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai dai ba su bar yin zunuban gidan Yerobowam ba, wanda ya sa Isra’ila ta aikata; suka ci gaba da yinsu. Haka ma, ginshiƙin Ashera ta kasance a tsaye a cikin Samariya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْدَهَكَ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ بَسُ جُويَا دَغَ بِنْ ذُنُبَنْ غِدَنْ يٜىٰرُواْبُواْوَمْ بَ، وَطَنْدَ يَسَا مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَبِے؞ عَمَّا سَيْ عَكَ بَرْ غُنْكِنَّنْ أَشٜىٰرَ أَ سَمَرِيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Duk da haka ba su rabu da zunuban gidan Yerobowam ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi. Sun aikata irin zunuban Yerobowam. Gunkiyan nan mai suna Ashtoret tana nan a Samariya.