2 Kings 14:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma Amaziya bai saurara ba, saboda haka Yehowash sarkin Isra’ila ya kai masa hari. Shi da Amaziya sarkin Yahuda suka fuskanci juna a Bet-Shemesh.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا أَمَظِيَ يَڧِ؞ سَيْ سَرْكِے يٜىٰهُواْوَشْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ يَهَوْرَ دُواْمِنْ شِ دَ سَرْكِے أَمَظِيَ نَ يَهُودَ سُڢُسْكَنْثِ جُونَ أَ بٜىٰتْ شٜىٰمٜىٰشْ نَيَنْكِنْ يَهُودَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma Amaziya bai ji ba. Sai Yehowash Sarkin Isra'ila ya tafi, ya shiga yaƙi da Amaziya, Sarkin Yahuza a Bet-shemesh ta Yahuza.