2 Kings 14:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Game da sauran ayyukan mulkin Yehowash, abin da ya yi da kuma nasarorinsa, haɗe da yaƙinsa da Amaziya sarkin Yahuda, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَوْرَنْ أَيُّكَنْ يٜىٰهُواْوَشْ دَ أَبِنْدَ يَيِ دَ إِيكُوانْ مُلْكِنْسَ دَ كُمَ يَدَّ يَيِ يَاڧِ دَ سَرْكِے أَمَظِيَ نَ يَهُودَ سُنَ أَرُبُوثٜىٰ عَثِكِنْ لِتَّڢِنْ تَارِيحِنْ سَرَاكُنَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sauran ayyukan Yehowash da dukan abin da ya yi, da ƙarfinsa, da yadda ya yi yaƙi da Amaziya, Sarkin Yahuza, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.