2 Kings 14:23 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Amaziya ɗan Yowash sarkin Yahuda, Yerobowam ɗan Yehowash sarkin Isra’ila ya zama sarki a Samariya, ya kuma yi mulki na shekaru arba’in da ɗaya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ شٜىٰكَرَا تَغُواْمَشَا بِيَرْ تَمُلْكٍ سَرْكِے أَمَظِيَ طَنْ يُواْوَشْ نَ يَهُودَ، سَيْ سَرْكِے يٜىٰرُواْبُواْوَمْ نَبِيُ طَنْ يٜىٰهُواْوَشْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ يَڢَارَ مُلْكِ أَ سَمَرِيَ؞ يَيِ مُلْكِ شٜىٰكَرَا أَرْبَعِنْ دَ طَيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A shekara goma sha biyar ta sarautar Amaziya ɗan Yowash Sarkin Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash Sarkin Isra'ila, ya ci sarauta a Samariya. Ya yi mulki shekara arba'in da ɗaya.