2 Kings 14:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk da haka bai kashe ’ya’yan masu kisan ba, bisa ga abin da yake a rubuce a Dokar Musa inda Ubangiji ya umarta, “Ba za a kashe iyaye saboda laifin ’ya’ya ba, ko kuma ’ya’ya saboda laifin iyayensu ba, kowa zai mutu don zunubansa.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا بَيْكَشٜىٰ یَیَنْ مُتَنٜىٰنْ نَنْبَ؞ يَيِ حَكَ بِسَغَ أَبِنْدَ عَكَ رُبُوتَ أَ كُواْيَرْوَرْ مُوسَٰى ثٜىٰوَ «بَذَاعَكَشٜىٰ إِيَايٜىٰ سَبُواْدَ ذُنُوبِنْ یَیَنْسُبَ، كُواْ عَثٜىٰ عَكَشٜىٰ یَیَ سَبُواْدَ ذُنُوبِنْ إِيَايٜىٰنْسُبَ؞ دُكْ مُتُمِنْدَ يَيِ ذُنُوبِ شِينٜىٰ ذَيْ مُتُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma bai kashe 'ya'yan masu kisankai ɗin ba, don ya bi abin da aka rubuta a littafin dokokin Musa, inda Ubangiji ya umarta cewa, “Kada a kashe iyaye saboda 'ya'ya, kada kuma a kashe 'ya'ya saboda iyaye, amma kowa zai mutu saboda laifin kansa.”