2 Kings 15:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Menahem ya tara kuɗin ne ta hanyar haraji a Isra’ila inda ya sa kowane attajiri ya ba da shekel hamsin don a ba sarkin Assuriya. Sa’an nan sarkin Assuriya ya janye, bai ƙara kasance a ƙasar ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے مٜىٰنَهٜىٰمْ يَسَامُواْ كُطِنْ دَغَ مَاسُ أَرْزِڧِ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ تَوُرِنْ سَا كُواْوَنّٜىٰنْسُ يَبِيَ هَرَاجِنْ أَظُرْڢَا حَمْسِنْ؞ وَنَّنْ كُطِنْ يَبَا سَرْكِنْ أَسُّرِيَ؞ سَيْ سَرْكِنْ أَسُّرِيَ يَكُواْمَ، بَيْ كَٰوُاْ يَاڧِ كَنْ ڧَسَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ بَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Menahem ya karɓi kuɗin daga mutanen Isra'ila, wato daga attajirai. Ya tilasta wa kowannensu ya ba da azurfa hamsin. Saboda haka Tiglat-filesar mai mulkin Assuriya ya koma ƙasarsa.