2 Kings 15:35 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk da haka, bai kawar da masujadan kan tudu ba; mutane suka ci gaba da yin hadaya da ƙona turare a can. Yotam ya sāke gina Ƙofar Bisa ta haikalin Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا دُكْدَهَكَ، بَعَكَوَرْدَ وُرَارٜىٰنْ سُجَّدَ دَ بَسُ دَاثٜىٰبَ، مُتَنٜىٰ سُنْيِ تَظُوَ سُنَ مِيڧَ هَدَايُ دَ هَدَايُنْ ڧُواْنَ تُرَارٜىٰ أَوُرَارٜىٰنْ؞ يُواْتَمْ يَكُمَ غِنَا ڧُواْڢَرْ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ وَدَّ تَكٜىٰ أَوُرِے مَڢِے ڟَيِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Duk da haka ba a kawar da wuraren tsafi na kan tuddai ba, amma mutane suka yi ta miƙa hadayu da ƙona turare a matsafai na kan tuddai. Shi ne ya gina ƙofa ta bisa ta Haikalin Ubangiji.