2 Kings 16:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka Uriya firist ya gina bagaden bisa ga tsarin da Sarki Ahaz ya aika masa daga Damaskus, ya kuma gama shi kafin Sarki Ahaz yă dawo.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عُرِيَ ڢِرِسْتِ يَغِنَ بَغَدٜىٰنْ دَيْدَيْ بِسَغَ عُمَرْنِنْ سَرْكِے أَهَظْ؞ عَكَ كُوَ غَمَ غِنِنْ كَاڢِنْ سَرْكِے أَهَظْ يَدَاوُاْ دَغَ دِمَشْڧُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Uriya firist kuwa, ya gina bagaden bisa ga yadda sarki Ahaz ya aika masa daga Dimashƙu. Uriya firist, ya gina bagaden kafin sarki Ahaz ya komo daga Dimashƙu.